KACRAN ta yi watsi da ƙirƙiro ƴansandan jihohi a Najeriya

0 Northerners - AREWARMU | Daily Post


Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kullen Allah ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su dakatar da shirin ƙirƙiro rundunar ƴansandan jihohi, tana mai cewa hakan na iya ƙara taɓarɓarewar tsaro maimakon magance matsalolin da ake fuskanta.

Da yake zantawa da BBC Hausa, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mohammed Khalil Bello, ya bayyana cewa ƙungiyar na fargabar wasu gwamnoni za su iya amfani da rundunar ƴansandan jihohi wajen musguna wa wasu al'ummomi, musamman makiyaya.

A cewarsa, akwai yiwuwar a yi amfani da rundunar domin nuna wariya ko ƙuntata wa wasu ƙabilu da al'ummomi, lamarin da ka iya haddasa sabbin rikice-rikice a sassa daban-daban na ƙasar.

Shugaban ƙungiyar ya kuma bayyana cewa mafi yawan jihohin Najeriya ba su da ƙarfin tattalin arzikin da zai ba su damar ɗaukar nauyin rundunar ƴansandan jihohi.

Ya ce ban da jihohi irin su Legas da wasu jihohin da ke samun kuɗaɗen man fetur, sauran jihohi na iya fuskantar ƙarin matsin kuɗi, wanda zai shafi biyan albashin ma'aikata da fansho.

Mohammed Khalil Bello ya ƙara da cewa idan aka kafa ƴansandan jihohi, wasu gwamnoni na iya rage tallafin da suke bai wa sojoji, 'yan sanda da jami'an tsaro na sa-kai, abin da ka iya raunana yaƙi da matsalar rashin tsaro.

Maimakon kafa rundunar ƴansandan jihohi, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara yawan jami'an tsaro na ƙasa, ta inganta albashi da walwalarsu, tare da samar musu da kayan aikin zamani domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Har ila yau, ƙungiyar ta jaddada muhimmancin amfani da tattaunawa, sasanci, afuwa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a matsayin hanyoyin da za su taimaka wajen rage matsalar rashin tsaro, musamman a yankin Arewa.

Batun ƙirƙiro ƴansandan jihohi na ci gaba da haifar da muhawara a Najeriya, inda wasu ke ganin zai taimaka wajen inganta tsaro, yayin da wasu kuma ke nuna damuwa kan yiwuwar amfani da rundunar ta hanyar da ba ta dace ba.

Tags :-

Post a Comment

0 Comments
Our website uses cookies to enhance your experience. Check Out
Ok, Go it!