Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan jagoran makiyaya na jihar, Alhaji Arɗo Risku, wanda aka kashe ranar Juma'a.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Tersoo Kula, ya fitar, gwamnan ya yi Allah wadai da kisan, tare da ba da umarnin kamo duk waɗanda ke da hannu a lamarin domin gurfanar da su a gaban shari'a.
Gwamna Alia ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su yi aiki tare da shugabannin al'umma da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya da hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.
Hakazalika, ya roƙi mambobin Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da sauran al'ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu tare da bai wa jami'an tsaro damar gudanar da bincike.
Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin Alhaji Arɗo Risku da kuma ɗaukacin mambobin ƙungiyar MACBAN, yana addu'ar Allah Ya jikansa da rahama tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
A nata ɓangaren, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Benue ta tabbatar da kama mutane 10 da ake zargi da hannu a kisan. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano cikakken yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da an hukunta duk masu hannu a kisan.
