Atiku Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Rajistar NDC, Ya Gargadi Kan Barazanar Jam'iyya Ɗaya

0 Northerners - AREWARMU | Daily Post


Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da abin da ya kira yunƙurin daƙile rajistar jam'iyyar NDC, yana mai zargin cewa hakan wani yunkuri ne na karkatar da Najeriya zuwa tsarin jam'iyya ɗaya ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya bayyana hakan ne bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi, ta soke hukuncinta na ranar 10 ga Disamba, 2025, wanda ya bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) umarnin yi wa jam'iyyar NDC rajista.

Mai shari'a Isah Dashen ya bayyana cewa ya zama dole a shigar da jam'iyyar PMP cikin shari'ar, saboda hukuncin na iya shafar muradunta. Saboda haka, kotun ta soke hukuncin da ta yanke a baya tare da buƙatar a ci gaba da shari'ar bisa sabon tsari.

A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Atiku Abubakar ya fitar, ya ce bai yi mamakin hukuncin ba, yana mai cewa akwai yunƙurin raunana jam'iyyun adawa domin bai wa Shugaba Tinubu damar sake tsayawa takara cikin sauƙi a zaɓen shekarar 2027.

Atiku ya yi gargaɗin cewa duk wani mataki da zai tauye damar 'yan ƙasa na shiga siyasa ko kafa jam'iyyun siyasa na iya yin illa ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ya jaddada cewa samun jam'iyyu masu yawa da damar shiga zaɓe cikin adalci na daga cikin ginshiƙan dimokuraɗiyya, yana mai cewa duk wani yunƙuri na takaita wannan 'yanci na iya haifar da rikice-rikicen siyasa da rashin kwanciyar hankali.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga ɓangaren shari'a da ya kiyaye 'yancin kansa da mutuncinsa, yana mai cewa kotuna su ne mafakar talakawa kuma ya kamata su kasance masu gudanar da adalci ba tare da son rai ko tsoma bakin siyasa ba.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin tarayya ko Hukumar INEC da ta mayar da martani kan kalaman da Atiku ya yi.

Tags :-

Post a Comment

0 Comments
Our website uses cookies to enhance your experience. Check Out
Ok, Go it!