An Kama Mutane Bakwai da Ake Zargin Jiga-Jigan Boko Haram da ISWAP Ne Bayan Dawowarsu Daga Hajji

0 Northerners - AREWARMU | Daily Post


Hukumomin Najeriya sun bayyana cewa sun kama mutane bakwai da ake zargi da kasancewa jiga-jigan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP, bayan dawowarsu daga aikin Hajjin shekarar 2026.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron sanya hannu kan sabuwar dokar shaidar ɗan ƙasa da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, an kama mutanen ne a Filin Jirgin Sama na Katsina a cikin makon da ya gabata, lokacin da suke dawowa daga aikin Hajji.

Ministan ya ce nasarar kamen ta biyo bayan bincike da tantance bayanan alhazan da suka halarci aikin Hajji daga sassa daban-daban na Najeriya.

Ya bayyana cewa a halin yanzu, waɗanda ake zargin suna hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, wadda ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken matsayinsu da kuma tabbatar da zarge-zargen da ake musu.

Tunji-Ojo ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da fasahohin zamani da haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen gano mutanen da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci, domin kare tsaron ƙasa da lafiyar al'umma.

Sai dai ya bayyana cewa bincike na ci gaba, kuma waɗanda aka kama za su ci gaba da cin moriyar haƙƙinsu a ƙarƙashin doka har sai an tabbatar da laifinsu a kotu.

Tags :-

Post a Comment

0 Comments
Our website uses cookies to enhance your experience. Check Out
Ok, Go it!