Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Iran ta nemi a gudanar da wata ganawa da Amurka a ranar Talata a birnin Doha na ƙasar Qatar, a wani yunkuri na rage tashin hankalin da ya biyo bayan musayar hare-hare tsakanin ƙasashen biyu a kwanakin baya.
Trump ya ce tattaunawar na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da tsagaita wuta da kuma ci gaba da hanyoyin diflomasiyya domin kauce wa ƙarin rikici a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya nuna fatan cewa bangarorin za su cimma matsaya da za ta taimaka wajen rage zaman ɗar-ɗar da ake ciki.
Fadar White House ta sanar da cewa manyan jami'an Amurka, Jared Kushner da Steve Witkoff, ne za su jagoranci tawagar da za ta halarci taron idan ya gudana. A cewar fadar shugaban ƙasar, ana kuma sa ran gudanar da wasu tattaunawa a gefe domin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyoyin da suka shafi tsaro da zaman lafiya.
Sai dai Iran ta musanta rahotannin cewa an shirya irin wannan ganawa a wannan makon. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce har yanzu ba a cimma matsaya kan ranar ko wurin gudanar da wata tattaunawa ba.
A cewarsa, masu shiga tsakani na ci gaba da tattaunawa da bangarorin domin nemo lokacin da ya dace, yana mai jaddada cewa babu wata yarjejeniya ta hukuma da aka kulla kan gudanar da taron a Doha.
Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa bambancin bayanan da ke fitowa daga Washington da Tehran na nuna cewa har yanzu akwai gibi a tsakanin bangarorin, duk da ƙoƙarin da ake yi na dawo da tattaunawa ta diflomasiyya.
Sun kuma yi nuni da cewa idan aka samu damar gudanar da ganawar, hakan na iya zama wani muhimmin mataki wajen rage tashin hankali da inganta dangantaka tsakanin ƙasashen biyu bayan watanni na rikici da musayar kalaman zafi.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga gwamnatin Qatar da ta tabbatar da cewa za ta karɓi bakuncin irin wannan taro, yayin da ake ci gaba da sa ido kan ci gaban tattaunawar.
