Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da tsoffin daraktocin matatun mai na gwamnati da ke Fatakwal da Warri bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatun mai da kuma halasta kuɗaɗen haram.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tsohon Manajan Daraktan Matatar Mai ta Fatakwal, Ahmed Adamu Dikko, da tsohon Manajan Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi Yisawu.
A cewar takardun kotun, hukumar na tuhumar Ahmed Adamu Dikko da laifuka 12, yayin da Jimoh Olasunkanmi Yisawu ke fuskantar tuhume-tuhume guda takwas. EFCC ta ce zarge-zargen sun haɗa da karɓar na goro daga hannun kamfanonin da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya ba kwangilar gyaran matatun, da kuma amfani da asusun banki wajen halasta kuɗaɗen da ake zargin an samo ba bisa ƙa'ida ba.
Hukumar ta bayyana cewa shari'ar na daga cikin binciken da take gudanarwa kan yadda aka kashe biliyoyin nairorin da gwamnatin tarayya ta ware domin gyaran matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna, waɗanda har yanzu ba su fara aiki yadda ake tsammani ba duk da kuɗaɗen da aka kashe a kansu.
Binciken EFCC ya mayar da hankali ne kan gano ko an yi amfani da kuɗaɗen gyaran matatun yadda ya kamata, tare da bin diddigin kadarori da kuɗaɗen da ake zargin an karkatar. Hukumar ta ce ta riga ta ƙwato biliyoyin naira da wasu kadarori daga hannun wasu tsoffin jami'an NNPC a wani ɓangare na binciken.
Masana harkokin tattalin arziki da yaƙi da cin hanci sun bayyana cewa wannan mataki na EFCC na iya ƙara ƙarfafa yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa, musamman a bangaren man fetur, wanda ke da muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin Najeriya.
Sai dai, a bisa tsarin doka, waɗanda ake tuhuma suna da haƙƙin a ɗauke su a matsayin marasa laifi har sai kotu ta tabbatar da laifinsu bayan kammala shari'a.
Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron shari'ar a kwanaki masu zuwa, yayin da jama'a ke sa ido kan sakamakon binciken da kuma matakan da za a ɗauka kan zarge-zargen.

.jpeg)