Iyayen ɗaliban da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ko ISWAP ne suka yi awon gaba da su yayin da suke rubuta jarabawar NECO a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Lassa, ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno, sun bayyana cewa suna cikin matsanancin tashin hankali tun bayan aukuwar lamarin.
Wasu daga cikin iyayen sun shaida cewa rayuwarsu ta sauya tun daga ranar da suka samu labarin harin, inda suka ce har yanzu ba su san inda 'ya'yansu suke ba ko kuma halin da suke ciki. Sun bayyana cewa rashin samun cikakken bayani daga hukumomi ya ƙara musu damuwa.
A cewarsu, abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne yadda har yanzu ba a bayyana a hukumance adadin ɗaliban da aka yi garkuwa da su ba, tare da rashin cikakken bayani kan yadda aikin ceto ke gudana.
Wani mazaunin garin Lassa, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce ya garzaya makarantar bayan jin ƙarar harbe-harbe, amma ya tarar da mutane na ta gudu domin tsira da rayukansu.
Ya ce duk da cewa 'ya'yansa sun tsira daga harin, iyalai da dama har yanzu ba su san inda 'ya'yansu suke ba. Ya ƙara da cewa sun zagaya asibitoci da wuraren da jami'an tsaro suka tara waɗanda aka ceto, amma ba su samu labarin wasu daga cikin ɗaliban ba.
A cewarsa, maharan sun yi awon gaba da kusan ɗalibai 50, sai dai daga baya jami'an tsaro sun samu nasarar ceto takwas daga cikinsu. Har yanzu ana ci gaba da neman sauran waɗanda suka ɓace.
Wata uwa da ɗiyarta ke cikin waɗanda ake nema ta bayyana cewa tun bayan da ta samu labarin harin ba ta sake samun nutsuwa ba. Ta ce sun tura 'ya'yansu makaranta ne domin su rubuta jarabawa cikin kwanciyar hankali, ba tare da tsammanin za su fuskanci irin wannan hari ba.
Ta yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya, tare da tabbatar da tsaron makarantu domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari.
Lamarin ya sake jawo hankalin al'umma kan matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar wasu yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya, musamman hare-haren da ake kai wa makarantu. Masana harkokin tsaro da na ilimi sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin ilimi domin kare rayuka da tabbatar da cewa ɗalibai na ci gaba da karatu ba tare da fargaba ba.
Iyalan waɗanda aka sace sun ce abin da suke fata a yanzu shi ne ganin an dawo da 'ya'yansu cikin ƙoshin lafiya, yayin da suke ci gaba da addu'o'i da kuma jiran sakamako daga ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi na cetonsu.
.jpeg)
