Sabon ƙudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya ya ƙara matsowa kusa da zama doka bayan Majalisar Dattawa ta amince da shi. Ƙudirin, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa Majalisar Tarayya, na ɗaya daga cikin muhimman sauye-sauyen da ake son yi a tsarin tsaron ƙasar.
Tun da farko, Majalisar Wakilai ta riga ta amince da irin wannan ƙudiri, sai dai akwai wasu bambance-bambance tsakanin sigar da ta amince da ita da wadda Majalisar Dattawa ta zartar.
Mataki na gaba shi ne kwamitin haɗaka na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai zai duba ƙudurorin biyu domin haɗa su zuwa tsari guda kafin a sake amincewa da shi.
Bayan haka, za a miƙa ƙudirin ga majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya. Bisa tanadin kundin tsarin mulki, aƙalla majalisun jihohi 24 ne dole su amince da shi kafin a aika wa shugaban ƙasa domin sanya hannu ya zama doka.
A halin yanzu, jam'iyyar APC mai mulki na da gwamnoni a jihohi 32 cikin 36 na ƙasar. Haka kuma, wasu jihohin da ba APC ke mulki ba, ciki har da Anambra da Abia, na da kyakkyawar alaƙa da gwamnatin tarayya.
Masu sharhin siyasa na ganin wannan na iya ƙara wa ƙudirin damar samun goyon bayan mafi yawan majalisun dokokin jihohi, wanda zai ba shi damar zama doka kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Sai dai batun kafa 'yan sandan jihohi na ci gaba da haifar da muhawara. Masu goyon bayan shirin na cewa zai taimaka wajen inganta tsaro da bai wa jihohi damar magance matsalolin da suka shafe su cikin sauri. A gefe guda kuma, masu adawa da shirin na nuna fargabar cewa ana iya amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba.
Ana sa ran muhawarar kan ƙudirin za ta ci gaba yayin da majalisun dokokin jihohi ke shirin fara nazari a kansa.
