Rundunar Operation Hadin Kai ta sanar da cewa dakarunta sun ceto ɗalibai da malamai 10 da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka sace bayan harin da suka kai a garin Lassa, da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
A wata sanarwa da mukaddashin jami'in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safiyar Litinin, lokacin da mayaƙan suka afka wa Makarantar Sakandaren Fasaha ta Lassa, inda ɗalibai ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO.
Sanarwar ta ce rundunar ta gaggauta tura dakaru tare da jiragen yaƙi domin gudanar da aikin ceto. Bayan artabu da mayaƙan a yankin Daggu, sojojin sun samu nasarar ceto mutum 10 ba tare da sun samu raunuka ba.
Rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da aikin neman mutum guda da ya rage a hannun maharan, tare da ƙoƙarin kamo waɗanda suka kai harin domin gurfanar da su a gaban kuliya.
A yayin fafatawar, sojojin sun kashe wasu daga cikin mayaƙan ISWAP, sannan sun ƙwace babura bakwai da ake zargin maharan sun yi amfani da su wajen kai harin da kuma ƙoƙarin tserewa.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wani soja da kuma ɗaya daga cikin jami'an sa-kai na JTF sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da mayaƙan.
Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da hare-hare da ayyukan ceto domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da ke fama da matsalar ta'addanci.
