An samu kusan mutane miliyan guda da suka shiga jerin masu mallakar miliyoyin dalar Amurka a shekarar 2025, abin da ya zama mafi girman ƙaruwar attajirai da aka gani cikin ƴan shekarun nan, a cewar sabon rahoton bankin UBS na Switzerland.
Rahoton ya bayyana cewa a kowace rana cikin shekarar 2025, sama da mutane 2,600 ne suka shiga sahun masu mallakar aƙalla dala miliyan guda. Wannan ya nuna yadda arziƙin ɗaiɗaikun mutane ya bunƙasa a sassa daban-daban na duniya.
Masana tattalin arziƙi sun danganta wannan ci gaba da hauhawar kasuwar hannayen jari, bunƙasar fasahar Artificial Intelligence (AI), da kuma ƙaruwa a dukiyar iyalai a ƙasashe da dama.
UBS ya kuma bayyana cewa jimillar arziƙin ɗaiɗaikun mutane ya ƙaru da kusan kashi 11 cikin ɗari a shekarar 2025, idan aka kwatanta da kashi 4.6 a 2024 da kuma kashi 4.2 a 2023.
Rahoton ya nuna cewa Amurka ce ta fi samun sabbin attajirai, inda fiye da mutane 440,000 suka shiga jerin masu mallakar miliyoyin daloli, abin da ya kai kusan rabin sabbin attajiran da aka samu a duniya.
Masana sun ce wannan ci gaba na nuna yadda fasahar AI da kasuwannin hada-hadar kuɗi ke ci gaba da samar da sabbin damammaki ga masu zuba jari. Sai dai sun gargadi cewa sauye-sauyen kasuwa na iya shafar darajar kadarori cikin gaggawa, don haka ya dace masu zuba jari su kasance masu yin taka-tsantsan.
