Kafofin Yaɗa Labaran Isra'ila Sun Soki Trump Bayan Yarjejeniyar Amurka da Iran

0 Northerners - AREWARMU | Daily Post




Wasu manyan kafofin yaɗa labarai na Isra'ila sun sauya matsayinsu kan Shugaban Amurka, Donald Trump, bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran.

Rahotanni sun nuna cewa kafofin da a baya suka kasance masu bayyana Trump a matsayin "babban abokin Isra'ila" sun fara sukar matakin, suna zargin cewa yarjejeniyar ta saɓa da muradun ƙasar Isra'ila.

Wannan sauyin ya fi bayyana a tashar Channel 14, wadda aka fi sani da goyon bayanta ga jam'iyyun masu ra'ayin mazan jiya da kuma Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

A cikin shirin maraice na tashar mai suna "The Patriots", masu sharhi sun bayyana damuwarsu kan yarjejeniyar, inda wasu suka kira matakin a matsayin "babbar cin amana" ga Isra'ila.

A baya dai, masu gabatar da shirin sun kasance daga cikin fitattun masu goyon bayan Trump. Daya daga cikinsu, Yinon Magal, ya sha fitowa sanye da hular da ke ɗauke da taken "Trump 2024", a matsayin nuna goyon baya ga tsohon shugaban Amurkan.

Masana harkokin siyasa sun ce sauyin da aka gani a wasu kafofin yaɗa labaran Isra'ila na nuna yadda yarjejeniyar Amurka da Iran ta haifar da muhawara tsakanin masu goyon bayan Isra'ila, musamman waɗanda ke ganin duk wata kusanci tsakanin Washington da Tehran na iya shafar manufofin tsaron Isra'ila.

Sai dai har yanzu gwamnatin Isra'ila da Fadar White House ba su fitar da cikakken bayani kan waɗannan sukar da wasu kafafen yaɗa labarai suka yi ba.

Tags :-

Post a Comment

0 Comments
Our website uses cookies to enhance your experience. Check Out
Ok, Go it!