Jega da Gambari Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar Rashin Tsaro da Lalacewar Tsarin Zaɓe a Najeriya
0
June 10, 2026
June 10, 2026
Wasu fitattun 'yan Najeriya, ciki har da tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Attahiru Jega, da tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ibrahim Gambari, sun yi gargaɗi kan irin barazanar da ƙasar ke fuskanta sakamakon ƙaruwar rashin tsaro, maguɗin zaɓe da kuma raunin cibiyoyin dimokuraɗiyya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar tare da wasu manyan masana da masu fafutukar kare dimokuraɗiyya, sun bayyana cewa Najeriya na fuskantar mawuyacin hali wanda ka iya jefa ƙasar cikin babban rikici idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba. Sun nuna damuwa kan yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar, tare da zargin cewa ana samun katsalandan a harkokin zaɓe da kuma raunin tsarin raba madafun iko tsakanin bangarorin gwamnati.
Jagororin sun kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ƙara sanya ido kan yadda gwamnati ke gudanar da harkokin mulki, tare da tabbatar da cewa an mutunta dokoki da kundin tsarin mulkin ƙasa. Sun jaddada cewa kare dimokuraɗiyya, tabbatar da sahihin zaɓe da kuma magance matsalar rashin tsaro su ne ginshiƙan da za su tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Sun buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnati, jam'iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da al'umma baki ɗaya, da su haɗa kai domin kare martabar dimokuraɗiyyar Najeriya gabanin zaɓukan shekarar 2027.
Tags :-
