Aƙalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a birnin Accra, babban birnin Ghana, bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a ranar Litinin. Ambaliyar ta haddasa gagarumar asarar rayuka da dukiyoyi, tare da lalata gidaje, motoci da sauran kadarorin al'umma.
Hukumar Kashe Gobara ta Ghana ta bayyana cewa jami'an ceto na ci gaba da gudanar da bincike a yankunan da ambaliyar ta fi shafa, tana mai gargadin cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Bidiyoyi da hotunan da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye manyan tituna da unguwanni, inda gidaje da motoci suka nutse gaba ɗaya. Ambaliyar ta fi shafar ƙananan yankuna da ke da matsalar magudanan ruwa, lamarin da ya haddasa tsaikon zirga-zirga da katse wasu hanyoyin sufuri.
Ko da yake ruwan ya fara raguwa a wasu wurare, mazauna yankunan da abin ya shafa na ci gaba da tantance irin asarar da suka yi. Wasu iyalai sun rasa gidajensu da dukiyoyinsu, yayin da wasu suka bar muhallansu domin neman mafaka a wurare masu aminci.
Shugaban Ghana, John Mahama, ya bayar da umarnin rusa dukkan gine-ginen da aka gina a hanyoyin ruwa, yana mai cewa irin waɗannan gine-gine na ƙara haddasa haɗarin ambaliya tare da jefa rayukan jama'a cikin barazana.
Ya kuma bayyana cewa sauyin yanayi na ci gaba da ƙara tsananta matsalar ambaliya, yana mai nuni da cewa an samu milimita 140 na ruwan sama cikin rana guda, adadin da ya zarce na shekarar da ta gabata.
Gwamnatin Ghana ta buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗari su koma wurare mafi tsaro, tare da gargadin direbobi da su guji hanyoyin da ruwa ya mamaye domin kauce wa haɗurra.
Ambaliyar ta kuma haifar da katsewar wutar lantarki a wasu sassan Accra, yayin da jami'an tsaro, masu aikin ceto da hukumomin agajin gaggawa ke ci gaba da kai dauki ga waɗanda bala'in ya shafa.
Masana muhalli sun bayyana cewa ƙasashen Afirka na ƙara fuskantar matsanancin sauyin yanayi, wanda ke haddasa yawaitar ambaliya, fari da sauran bala'o'i. Sun yi kira ga gwamnatoci su ƙara saka hannun jari wajen inganta magudanan ruwa, tsara gine-gine bisa ƙa'ida da kuma ɗaukar matakan da za su rage illar sauyin yanayi.
