Masu aikin ceto na ci gaba da laluben ɓaraguzan gine-gine a sassa daban-daban na Venezuela bayan wata mummunar girgizar ƙasa da ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 235 tare da jikkata fiye da mutum 4,300.
Rahotanni sun nuna cewa girgizar ƙasar guda biyu masu ƙarfin maki 7.2 da 7.5 a ma'aunin Richter sun afku ne da yammacin ranar Laraba, inda suka haddasa rugujewar gine-gine, katse hanyoyin sufuri da kuma jefa dubban mutane cikin matsananciyar fargaba.
A biranen Caracas da La Guaira, jami'an ceto na ci gaba da aikin neman waɗanda ake zargin sun makale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe. Shaidu sun bayyana cewa ana ci gaba da jin kukan neman taimako daga wasu da ake kyautata zaton suna raye a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen.
Shugaban Majalisar Dokokin Venezuela, Jorge Rodríguez, ya bayyana cewa akalla gine-gine 250 ne suka rushe sakamakon girgizar ƙasar, inda mafi yawan lalacewar ta faru a birnin La Guaira. Rahotanni sun kuma tabbatar da rushewar wani otal mai hawa goma, wanda ya zama tarkace gaba ɗaya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Diosdado Cabello, ya ce ba La Guaira kaɗai ba ce ta fuskanci mummunar barna, domin an samu asarar gine-gine da dama a Caracas da kuma jihohin Trujillo, Yaracuy, Carabobo, Aragua da Miranda.
Hukumomin ƙasar sun ayyana dokar ta-baci a yankunan da abin ya fi shafa tare da tura jami'an ceto, sojoji da ma'aikatan lafiya domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa. Haka kuma an buɗe cibiyoyin wucin gadi domin ba da mafaka ga dubban mutanen da suka rasa gidajensu.
Masana sun bayyana cewa girgizar ƙasa mai irin wannan ƙarfi na iya ci gaba da haifar da ƙananan girgizar ƙasa (aftershocks), abin da ke ƙara haɗarin rugujewar sauran gine-ginen da suka riga suka samu matsala.
Ƙungiyoyin agaji na cikin gida da na ƙasa da ƙasa sun fara isar da kayan agaji, abinci, ruwa da magunguna ga yankunan da bala'in ya shafa, yayin da ake ci gaba da ƙididdige asarar rayuka da dukiyoyi.
