Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Kaduna Ta Arewa, Hon. Mohammed Bello El-Rufai, ya samu tikitin tsayawa takarar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ba tare da wani ya kalubalanci takararsa ba a zaben fidda gwani da aka gudanar ranar Asabar.
El-Rufai, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ADC a farkon watan Mayu, ya zama zababben dan takarar jam'iyyar domin wakiltar mazabar Kaduna Ta Arewa a zaben shekarar 2027.
Bayan nasarar da ya samu, Mohammed Bello El-Rufai ya nuna godiyarsa ga shugabannin jam'iyyar, magoya baya da kuma wakilan da suka kada kuri'a, inda ya bayyana cewa wannan nasara wani babban nauyi ne da ya rataya a wuyansa na ci gaba da yi wa al'umma hidima.
Ya kuma yabawa sauran masu neman takarar, musamman Hon. Nazifi Jibo, saboda hadin kai da suka nuna wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar. El-Rufai ya yi alkawarin gudanar da yakin neman zabe daga gida zuwa gida domin neman goyon bayan al'ummar mazabar kafin babban zaben 2027.
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ADC ta ayyana tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar domin tunkarar zaben 2027.
Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Bello El-Rufai ya samu kuri'u 7,727 a zaben fidda gwanin, lamarin da ya tabbatar da cikakken goyon bayan da yake da shi a cikin jam'iyyar a mazabar Kaduna Ta Arewa.
