Sirri 5 Na Zuciyar Namiji A Soyayya


Sau da yawa ana ganin namiji a matsayin mai ɓoye soyayyarsa, amma a gaskiya yana da abubuwa masu yawa da yake ɓoyewa a cikin zuciyarsa Ga sirri 5 na zuciyar namiji da ya dace mace ta fahimta:

1. Namiji yana son a girmama shi fiye da komai

Ko da yana ƙaunar mace sosai, rashin girmamawa na iya rage masa sha’awa. Kalma ɗaya ko hali kaɗan na iya shafar zuciyarsa fiye da yadda mace ke zato.

2. Namiji yana ɓoye damuwarsa

Yawancin maza ba sa iya faɗin abin da ke damunsu. Yakan yi shiru ne ba don bai damu ba, sai don ba ya son nuna rauninsa

3. Yana son a yarda da ƙoƙarinsa

Ko da ƙananan abubuwa yake yi, yana son a yabamashi. Godiya da yabawa suna ƙara masa ƙwarin gwiwa da ƙauna.

4. Namiji yana tsoron gazawa a soyayya

Duk da nuna jarumtaka, a zuciyarsa yana tsoron kada ya cutar da wadda yake so ko ya kasa ba ta farin ciki.

5. Idan ya gaskata soyayya, yana ba da zuciyarsa gaba ɗaya

Namiji idan ya yanke shawarar soyayya ta gaskiya, yana iya sadaukarwa sosai. Amma idan aka ci amanarsa, yana wahalar mantawa.

Bayan haka

Fahimtar zuciyar namiji na taimaka wa mace ta gina soyayya mai ƙarfi da kwanciyar hankali. Soyayya ba faɗa kaɗai ba ce—fahimta, girmamawa da haƙuri su ne ginshikinta

Post a Comment

0 Comments