Life π§¬
Abubuwa guda uku da kake yi suna kawo faduwa a rayuwarka
Ga abubuwa guda uku da mutane da yawa suke yi suna jawo faduwa a rayuwa, ko a kasuwanci, soyayya, ko ci gaban kai:
1. Rashin tsari da buri mai kyau
Idan kana rayuwa ba tare da tsari ba, baka san inda kake nufi ba.
Duk wanda bai saka buri a rayuwarsa ba, zai yi ta zagaye yana wahala amma babu cigaba.
π Rayuwa ba ta tafi da sa’a kawai, tsari da manufa suke kai mutum nasara.
2. Yawan bayyana sirrin ka ga kowa
FaΙin shirin ka, kudin ka, ko matsalarka ga kowa
yana jawo hassada, shisshigi, da raunana zuciya.
π Ba kowa ne yake maka fatan alheri ba,
ka rike sirrinka, ka yi aiki cikin shiru.
3. Rashin hakuri da gaggawa
Mutane da yawa suna so nasara cikin gajeren lokaci.
Idan basu gani nan take ba, sai su fasa.
π Duk abin kirki yana bukatar lokaci, hakuri, da juriya.
Wanda bai daure ba, yawanci yana faduwa a hanya.
π Ka tuna:
Faduwa ba ko yaushe take zuwa daga waje ba —
yawanci daga abubuwan da muke yi da kanmu take farawa.
Post a Comment
0 Comments