Love ❤️🩹
Sirri 7 Da Ke Sa Soyayya Ta Dore
Soyayya abu ne mai daɗi, amma ba kowace soyayya ce take dawwama ba. Wasu sukan fara da zafi, amma su ƙare da sanyi. Don haka, me yake sa soyayya ta dore har ta kai ga aure ko rayuwa mai albarka? Ga sirri guda 7 da suke taimakawa soyayya ta tsaya daram 💖
1. Gaskiya da Amana
Gaskiya ita ce ginshiƙin soyayya. Idan babu gaskiya, soyayya tana rushewa. Ka faɗi gaskiya komai zafinta, domin ƙarya tana karewa . Amana kuma tana sa zuciya ta nutsu.
2. Tattaunawa Mai Kyau
Soyayya ba ta rayuwa da shiru. Ku saba tattaunawa cikin ladabi, ku faɗi abin da ke damunku ba tare da cin mutunci ba. Magana tana gyara abin da zuciya ba za ta iya ɗauka ita kaɗai ba.
3. Hakuri da Juriya
Mutum daya baya cika Hakuri yana taimaka maka ka fahimci kuskuren masoyinka, ka gyara ba tare da tashin hankali ba. Soyayya ba ta dorewa sai da hakuri.
4. Girmama Juna
Idan babu girmamawa, babu soyayya. Kada ka raina ra’ayin masoyinka, ko ka wulakanta shi a gaban mutane. Girmamawa tana ƙara ƙauna a zuciya.
5. Kula da Jin Daɗin Juna
Ka damu da farin cikin masoyinka kamar naka. Ƙananan abubuwa kamar tambayar “ya kake?” ko “yaya jikinki?” na iya ƙara soyayya fiye da kyauta mai tsada.
6. Gujewa Zargi da Kishi Fiye da Kima
Kishi mai yawa yana lalata soyayya. Kada ka riƙa zargi ba tare da hujja ba. Amincewa da juna na sa zuciya ta huta.
7. Tsoron Allah
Soyayya da aka gina bisa tsoron Allah tana da albarka. Idan kowa yana tsoron Allah, ba zai cutar da ɗayan ba, kuma soyayya za ta zama mai tsafta da dorewa.
Bayan Haka
Soyayya ba kawai kalmomi ba ce, aiki ce. Idan aka haɗa gaskiya, hakuri, girmamawa da tsoron Allah, to soyayya za ta dore har abada in sha Allah 🤍

Post a Comment
0 Comments