Business 🏭
Sirri 5 Na Samun Riba A Kasuwanci
Sirri 5 Na Samun Riba A Kasuwanci
Kasuwanci ba wai saye da sayarwa kawai ba ne. Idan kana son ka ga riba mai ɗorewa, dole ka san wasu sirrika da manyan ‘yan kasuwa ke amfani da su. Ga sirri guda 5 da za su taimaka maka ka ƙara riba a kasuwancinka.
1. Sanin Abokin Ciniki (Customer)
Idan baka san su waye kake kasuwa dasu ba zaka sha wahalar samun riba.
Ka tambayi kanka:
Su waye kwastomominka?
Me suke bukata?
Nawa suke iya biya?
Idan ka fahimci bukatarsu, zaka iya kawo kaya ko tsari da ya dace da su – hakan zai ƙara yawan siye.
2️⃣ Ƙaramar Riba, ka siyar
Wasu ‘yan kasuwa suna sa riba mai yawa a kaya guda, hakan yana rage yawan masu siya.
Wani lokaci ƙaramar riba amma da yawan siyarwa na kawo kuɗi fiye da riba mai yawa a kaya kaɗan.
👉 Misali: Riba ₦500 a kaya 100 ta fi riba ₦2,000 a kaya 10.
3. Rage Asara wajen kashe kudin banza
Riba tana ƙaruwa idan asara ta ragu.
Kada ka sayi kaya da ba su tafiya.
Kula da rubuta shiga da fita.
Guji bashin da ba shi da tabbas.
Idan ka rage kuɗin banza, zaka ga riba tana ƙaruwa ba tare da ka ƙara farashi ba.
4. Kyakkyawar Mu’amala
Mutane suna dawowa inda aka girmama su.
Yi magana cikin mutunci.
Ka zama mai gaskiya.
Ka saurari korafin kwastoma.
Abokin ciniki ɗaya mai farin ciki zai iya kawo maka wasu 3–5.
5. Tallatawa (Marketing)
Ko kaya mai kyau ne, idan ba a san da shi ba – ba za a siya ba.
Yi amfani da WhatsApp status
Facebook, TikTok, ko Instagram
Ka saka hotuna masu kyau
Ka rubuta bayanin da ke jan hankali
Tallatawa ita ce zuciyar kasuwanci.
✅ Karin bayani
Samun riba a kasuwanci ba sa’a ba ne, tsari ne.
Idan ka haɗa: sanin kwastoma, rage asara, kyakkyawar mu’amala, da kuma tallatawa mai kyau – zaka ga canji a kasuwancinka.
👉 Ka fara amfani da waɗannan sirrika daga yau, ka lura da bambanci cikin watanni kaɗan.