Shawara 5 Ga Masu Fara Sana'a Da Ƙaramin jari


Fara sana’a ba lallai sai da jari mai yawa ba. Abin da yafi muhimmanci shi ne tunani mai kyau, jajircewa, da hakuri. Ga shawarwari guda biyar da zasu taimaka maka ka tashi tsaye ko da kana da ƙananan kuɗi 👇

1. Fara da abin da ka sani

Ka zaɓi sana’ar da ka fahimta ko ka taba yi. Ilimi da kwarewa nasa asara ta rage a tafiyar fako
Misali: Idan ka iya gyaran waya, ka fara da hakan maimakon ka shiga abin da baka sani ba.

2. Kada ka raina ƙaramar riba

Ƙananan riba idan ta zama kullum, tana girma. Kada ka tsaya jiran babbar riba tun farko.

Darasi: Riba kaɗan sai hakuri matakin nasara.

3. Ka rika juyar da riba cikin sana’a
Kada ka cinye duk ribar da ka samu.
 Ka rika mayar da wani kaso don bunƙasa sana’ar.
Darasi: Sana’a tana girma ne da abin da ka saka mata.

4. Ka nisanci bashi mara tsari

Bashi ba laifi bane, amma idan babu tsari zai rushe sana’a. Ka fara da abin da kake da shi.
Darasi: Sana’ar da ta fara a hankali tafi dorewa.

5. Ka kasance mai gaskiya da hakuri

A kasuwanci, gaskiya tana jawo kwastoma, hakuri kuma yana kai ka ga buri.

Darasi: Gaskiya + hakuri = kwanciyar hankali da albarka.

Bayan haka

Kar ka jira sai ka tara kuɗi masu yawa kafin ka fara. Ka fara yanzu da kaɗan, ka gina a hankali, ka zama abin koyi gobe.
“Babbar sana’a ta fara ne da ƙaramin mataki.”