Shawara 4 Ga Manyan ’Yan Kasuwa


A duk lokacin da kasuwanci ya fara girma, kalubale ma suna kara yawa. Abin da yake taimakawa manyan ’yan kasuwa su ci gaba da samun nasara shi ne fahimtar wasu muhimman ka’idoji da kuma bin su da gaske. Ga shawarwari guda 4 da suka dace da duk wanda kasuwancinsa ya riga ya wuce matakin ƙanana.

1. Ka Gina Tsari, Kada Ka Dogara Da Tafiya Kai kadai

Yawancin ’yan kasuwa suna faduwa ne lokacin da kasuwancinsu ya girma amma har yanzu suna son su rika yin komai da kansu. Babban kasuwanci yana bukatar tsari, dokoki, da ma’aikata masu kwarewa.
Idan ka gina tsari mai kyau, kasuwancin zai iya tafiya ko da ba ka nan.

2. Ka Raba Kudin Kasuwanci Da Na Rayuwa

Wannan kuskure ne da yawa daga manyan ’yan kasuwa ke yi. Duk da kasuwanci ya girma, idan kana haɗa kudin kasuwanci da na rayuwarka, to kana gina matsala a gaba.
Ka tanadi albashi ko alawus dinka, sauran kudin su ci gaba da zama jari.

3. Ka Zuba Jari A Ilimi Da Sabbin Dabara

Duniya tana canzawa kullum. Kasuwancin da ya yi nasara jiya, ba lallai ya yi nasara gobe ba idan ba ka sabunta kanka ba.
Ka rika:
Koyo daga sauran manyan ’yan kasuwa
Halartar taruka (seminars)
Bin sabbin hanyoyin talla da fasaha
Ilimi shi ne abin da ke sa babban kasuwanci ya daɗe.

4. Ka Gina Suna Mai Kyau (Brand & Aminci)

A matakin manyan ’yan kasuwa, suna ya fi riba muhimmanci. Idan mutane sun amince da kai:
Za su dawo
Za su kawo sababbin kwastomomi
Za su tsaya tare da kai ko a lokacin ƙalubale
Aminci, gaskiya, da cika alkawari su ne ginshiƙan babban suna.

Bayan haka 👉 

Kasuwanci ba wai girman jari kaɗai ba ne, tunani da tsari ne ke sa kasuwanci ya zama babba kuma ya daɗe. Idan kai babban ɗan kasuwa ne, ka tambayi kanka:

“Shin kasuwancina zai iya tafiya ba tare da ni ba?”
Idan amsar ita ce eh, to kana kan hanya mai kyau.